VOA Hausa
LAFIYARMU: Hira Da Dr. Ibrahim Bello, Babban Jami’i A Sashen Jini Na Asibitin Kasa Dake Abuja
- Title
- LAFIYARMU: Hira Da Dr. Ibrahim Bello, Babban Jami’i A Sashen Jini Na Asibitin Kasa Dake Abuja
- Runtime
- 3:20
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Dr. Ibrahim Bello, babban jami’i a sashen jini na asibitin kasa da ke Abuja yayi mana karin bayani a game da cutar ta Anemia da hanyoyin kare kai.
- Title
- #TASKARVOA: Karin haske akan wasu dalilai da suka sa girgizar kasar a Morocco ta yi muni sosai
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Majalisar dokokin Ghana ta amince da wani kudurin doka da za ta haramta zargin mutane da maita; Mutane da dama a sassan Najeriya su na sukar shirin gwamnatin kasar na raba tallafin rage radadin rayuwa, da wasu rahotanni
- Title
- Adadin Wadanda Suka Mutu A Derna Zai Kai 18,000-20,000 - Kukumomin Libya
- Runtime
- 0:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Abdulmenam al-Ghaithi, magajin garin Derna, daya daga cikin garuruwan Libya da ambaliyar ruwa ta fi shafa, ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa adadin wadanda suka mutu a birnin zai iya kaiwa mutane 18,000-20,000, bisa la'akari da irin barnar da aka samu sakamakon wannan mummunan lamari. #libya #eu #aid #disaster #VOAHausa
- Title
- TASKAR VOA: Wani abu da ke kara bayyana shi ne yadda mutane ke nuna goyon baya ga mulkin soja
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta ware sama da Naira miliyan 800 don gudanar da auren mutane 1,800 lokaci daya a karkashin wani shirinta na aurar da zaurawa; Wani matashi injiniya a Maiduguri ya na kera keke mai amfani da lantarki don baiwa mutane samun saukin zirga-zirga, da wasu rahotanni
- Title
- LAFIYARMU: Abubuwan Da Ke Haifar Da Matsalar Rudewar Ciki
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce ana kamuwa da cututtuka sama da 200 ta hanyar cin abincin da ke dauke da kwayoyin cutar bacteriya, biros ko kuma sinadarai masu illa.
- Title
- Yadda ake ci gaba da nuna kyama ga sojojin kasar Faransa a Nijar
- Runtime
- 2:44
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Biyo bayan cikar wa'adin wata daya da sojoojin Nijar suka baiwa kasar Farasa domin ta kwashe dakarunta a kasar,'yan kasar tanNijar sun shirya wani zaman dishin na yadda hali yayi a birnin Yamai.
- Title
- #TASKARVOA: Juyin mulki da takunkumin ECOWAS ya sa al’amura a Nijar na ci gaba da tafiyar hawainiya
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya RIFAN, ta ce sama da masana’antun shinkafa 50 a jihar Kano aka rufe saboda karancin shinkafa a fadin kasa; Wasu manoma mata da miji ‘yan asalin Najeriya mazauna Amurka suna amfani da fasaharsu wajen inganta sana’arsu ta noma a jihar Maryland, da wasu rahotanni
- Title
- Matakan Tabbatar Da Wanzuwar Zaman Lafiya Da Gwamnatin Jihar Borno Ke Dauka
- Runtime
- 3:31
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- A wani mataki na tabbatar da dorewar zaman lafiya a jihar Borno mai fama da rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, gwamnati ta raba ababen hawa ga jami’an tsaro da ‘yan sa-kai a jihar.
- Title
- Yadda Batun Kula Da Muhalli Ya Zama Jigo A Bikin Ranar Matasa ta Duniya A Jihar Filato
- Runtime
- 3:56
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Tattala muhalli ta hanyar dasa bishiyoyi da kula da shuke-shuke, shi ne abin da ya zama jigo a shagulgulan bikin ranar matasa ta duniya a jihar Filaton Najeriya, wanda aka yi a ranar 12 ga watan Agustan 2023.
- Title
- Sakon Shugaba Ali Bongo yayin da ake ci gaba da tsare shi a gidansa
- Runtime
- 0:47
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shugaban Gabon Ali Bongo da sojojin kasar suka ce sun kifar da gwamnatinsa, ya yi kira ga "abokan kasar" da su fito su yi magana kan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Labara.
AP
- Title
- Taron kungiyar Zumunta na shekara-shekara 2023
- Runtime
- 7:11
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Kowace shekara, ’yan kungiyar Zumunta suna haduwa a wuri guda domin sada zumunta da kuma duba yiwuwar yadda zasu taimaka wa juna da kuma yadda zasu bada nasu gudunmawa wajen cigaban Najeriya. Sannan yin hakan yana taimaka wa yaran da suke Haifa wajen fahimtar al’adu da mahimmancin hadin kai da zaman lafiya.
- Title
- #TASKARVOA: Wani binciken na nuni da kashi 30 cikin 100 na matan Najeriya suna fuskantar cin zarafi
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Shugaban Ghana Nana Akufo Addo, ya sanya hannu kan kudirin dokar da Majalisar Dattawan Ghana ta amince na soke hukuncin kisa; Shugabannin mata na Fulani sun ce mata za su iya taka muhimmiyar rawa wajen rage takun saka tsakanin manoma da makiyaya, da wasu rahotanni
- Title
- LAFIYARMU: Cututtukan Idanu Dake Haifar Da Rashin Gani Ko Makanta
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Glacoma shike kan gaba wajen haifar da makantar da idanu basa a sake gani na (dindindin), sannan itace abu na biyu dake haifar da makanta.
- Title
- #TASKARVOA: Yanayin Nijar Ya Haifar Da Matsalolin Tattalin Arziki Ga Al'ummomin Kan Iyakokin Kasar
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Gwamnatin Kenya na samar da matsugunai ga wadanda suka tsira daga safarar mutane; Ficewar Rasha daga yarjejeniyar fitar da Hatsi ta Bahar Maliya na shafar kokarin Najeriya na dogaro da kai, da wasu rahotanni
- Title
- LAFIYARMU: A Nijar Ayyukan Jinkai Ya Ragu Sakamakon Jerin Takunkumai Da ECOWAS Ta Kakkaba
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- A Nijar, inda aka samu juyin mulki sannan aka kakaba wa kasar jerin takunkumai, ayyukan kungiyoyin jinkai ya ragu sossai, lamarin da ya jefa al’ummomin da suke ba su tallafi cikin takaici.
- Title
- Blinken ya ce har yanzu akwai 'hanya ta diflomasiyya' da za a bi don kawar da juyin mulkin Nijar
- Runtime
- 0:16
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce har yanzu yana ganin akwai hanyar diflomasiyya da za a bi don kawo karshen juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar, yayin da kungiyar kasashen yammacin Afirka ke ci gaba da nuna matsin lamba kan shugabannin sojoji a Yamai. "Muna ci gaba da mai da hankali sosai kan diflomasiyya don samun sakamakon da muke so, wato na dawo da tsarin mulki, kuma na yi amannar cewa, ana ci gaba da samun hanyoyin diflomasiyya wajen cimma wannan sakamakon," Blinken ya shaida wa manema labarai.
#voahausa #Niger #Nigercoup #africacoups #MohamedBazoum #WagnerGroup #Russie #coupdetat #EtatsUnis #USA #CEDEAO #Tchad #BurkinaFaso #Mali #ECOWAS #Bazoum #Blinken #shorts #short #videoshort #videoshorts
Ku Bibiyi Shafin VOA Hausa YouTube: https://bit.ly/3Gcp7en
- - - - - -
Karin bayani akan VOA Hausa: https://www.voahausa.com
Karin bayani akan Facebook: https://www.facebook.com/voahausa
Karin bayani akan I...
- Title
- Sojojin Juyin Mulkin Nijar Sun Sha Alwashin Hukunta Bazoum | VOA Hausa
- Runtime
- 0:30
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Gwamnatin mulkin sojan Nijar a ranar Litinin ta sha alwashin gurfanar da hambararren shugaban kasar Mohammed Bazoum a kotu bisa laifin "cin amanar kasa" da kuma yi wa sha’anin tsaron kasa zagon kasa.
Wata sanarwa da shugaban mulkin sojin kasar, Kanar Major Amadou Abdramane ya karanta a gidan talabijin na kasar ta ce, ya zuwa yanzu gwamnatin sojin kasar ta tattara hujjojin da suka dace domin gurfanar da Bazoum da kuma “hadin wasu mutane na cikin gida da na waje.”
Yayin da yake gabatar da jawabin, Abdramane ya kuma ce rundunar sojin ta Nijar ta yi Allah wadai da matakan da kungiyar ECOWAS ta dauka na yunkurin da ta yi na mayar da Bazoum kan karagar mulki tare da gabatar da "takunkuman karya tattalin arziki," kan juyin mulkin.
Takunkumin ECOWAS ya hana “kasar samun magunguna, kayan abinci na yau da kullun da kuma wutar lantarki,” in ji Abdramane.
#voahausa #africa #niger #nigercoup #africacoups #MohamedBazoum #WagnerGroup #Ra...
- Title
- Gwamnatin Soji Ta Nijar Yanzu Ta Amince Da Zaman Sulhu Tsakaninta Da ECOWAS - Sheikh Bala Lau
- Runtime
- 4:21
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Da alamar wata kofa ta bude don tattaunawa tsakanin kungiyar ECOWAS da sojojin da su ka yi juyin mulki a janhuriyar Nijar da sauran masu ruwa da tsaki. Wannan ya biyo bayan ziyarar shiga tsakani da wasu manyan malaman Najeriya su ka kai.
- Title
- ECOWAS Gathers for Key Summit on Niger Coup | VOA Hausa
- Runtime
- 0:35
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shugaban Najeriya Bola Tinubu, kuma Shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, ya bude taron kungiyar kasashen yankin kan batun Nijar, inda ya yi nuni da muhimmancin ba da fifiko kan bin matakin diflomasiyya wajen mayar da kasar bisa tsarin doka da oda bayan juyin mulkin ranar 26 ga watan Yuli.
“Muna ba da fifiko kan tattaunawa ta diflomasiyya wacce ita ce ginshikin yadda muke fatan tunkarar lamarin,” in ji Tinubu.
A baya, kungiyar ECOWAS ta baiwa shugabannin mulkin sojan na Nijar mako guda su maido da hambararren Shugaban kasar Mohamed Bazoum, ko kuma su fuskanci yiwuwar amfani da karfin soji.
Amma jagororin juyin mulkin dai sun ci gaba da bijirewa wa'adin da aka ba su, inda suka nada sabuwar gwamnati tare da kin amincewa da tarukan kungiyar ECOWAS da na Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Afirka suka yi.
#voahausa #africa #niger #nigercoup #africacoups #MohamedBazoum #WagnerGroup #Rasha #coupdet...
- Title
- ECOWAS: An Gwammance Amfani Da Diflomasiyya Wajen Warware Ricikin Juyin Mulkin Nijar | VOA Hausa
- Runtime
- 0:22
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shugaban Najeriya Bola Tinubu da kungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka da yake shugabanta sun gwammace a sasanta ta hanyar diflomasiyya da lumana fiye da amfani da karfin sojoji game da juyin mulkin soji a Nijar, in ji kakakinsa Ajuri Ngelale a ranar Talata.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja babban birnin Najeriya, Ngelale ya ce kungiyar za ta gwammace amfani da jituwar da aka cimma ta hanyar diflomasiyya, ta hanyar lumana, maimakon kowane irin mataki daban, wanda kuma zai zama matsayin da za a ci gaba da shi.
Ya kara da cewa wannan zabin na iya canzawa, ya danganta da kudurorin da za a tattauna kansu nan gaba a taron ECOWAS da za a yi ranar Alhamis.
#voahausa #africa #niger #nigercoup #africacoups #MohamedBazoum #WagnerGroup #Rasha #coupdetat #france #CEDEAO #Chad #BurkinaFaso #Mali #ECOWAS #Bazoum #Tinubu #BolaTinubu #nigeria
Ku Bibiyi Shafin VOA Hausa YouTube: https://bit.ly/3Gcp7en
- - - - - -
Karin bayani ...
- Title
- Dubban Magoya Bayan Juyin Mulki A Jamhuriyar Nijar Sun yi Gangami A Dandalin Wasa Na Kasa| VOA Hausa
- Runtime
- 0:49
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Dubban magoya bayan juyin mulkin da soja su ka yi a Nijar sun yi gangami jiya Lahadi a wani dandalin wasa da ke Yamai babban birnin kasar domin nuna adawa da wa'adin da kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayar da cewa a sake tare da maido da shugaban kasar da aka zaba a dimokaradiyyance, Mohamed Bazoum, kan karagar mulki.
Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka din ta yi barazanar daukar matakin soji. Sai dai majalisar dattawan Najeriya mai makwabtaka da Najeriya ki goyon bayan shirin, inda ta bukaci Shugaban Najeriya, kuma Shugaban kungiyar ta ECOWAS a ranar Asabar da ya binciko wasu hanyoyin da za a yi amfani da su a maimakon amfani da karfi.
Kungiyar ta ECOWAS dai na iya ci gaba da laluba mafita, dayake akan dau mataki na karshe ne bayan mambobin kungiyar sun cimma jituwa, to amma gargadin da aka yi a jajibirin cikar wa’adin ya haifar da tambayoyi game da makomar batun shiga tsakani. - AP
#voahausa #africa #niger #Nijar...
- Title
- Jakadan Nijar A Amukra Ya Mana Karin Haske Akan Dambarwar Dake Faruwa Nijar
- Runtime
- 5:38
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Akan wannan dambarwa dake faruwa a Nijar, mun samu tattaunawa da jakadan Nijar din anan Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri.
- Title
- Taron Gaggawa Na ECOWAS Da Matakan Da Ta Dauka
- Runtime
- 2:47
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- A wani taron gaggawa da ta yi a Abuja a kan juyin mulkin a Nijar, kungiyar ECOWAS ta bai wa sojojin kasar wa’adin mako guda da su mayar da gwamnatin Mohamed Bazoum ko kuma ta dauki dukkan matakin da ya dace – wanda ya hada da yiwuwar amfani da karfin soji.
- Title
- Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Da Na 'Yan Nijar Mazauna Najeriya Akan Juyin Mulkin
- Runtime
- 5:42
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- To mutane a fadin duniya dai na ci gaba da tsokaci a kan juyin mulkin da aka yi a Nijar, mun kuma samu jin ra’ayoyin wasu ‘yan kasar ta Nijar da kuma na wasu ‘yan Nijar mazauna Najeriya.
- Title
- Abinda Ke Kawo Juyin Mulki A Wasu Kasashe - Bazoum 2021
- Runtime
- 3:35
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Mun duba wata hira ta musamman da Muryar Amurka ta yi da Shugaba Mohamed Bazoum a 2021, inda shugaban ya bayyana ra'ayinsa akan abinda ke kawo juyin mulki a wasu makwabtan kasar.
- Title
- Sojojin Faransa Sun Taimakawa Fararen Hula Da Ake Kwashe Su Daga Nijar | VOA Hausa
- Runtime
- 0:21
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Yan kasar Faransa da ‘yan kasashen ketare sun hallara ranar Talata a filin jirgin saman Diori Hamani da ke babban birnin Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da Faransa ke shirin kwashesu daga kasar.
Kasashen Faransa da Italiya da Spain sun sanar da kwashe 'yan kasarsu da sauran 'yan kasashen Turai daga Nijar, saboda fargabar cewa suna cikin hadarin makalewa yayin juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya samu goyon bayan wasu kasashen yammacin Afirka uku da wasu sojojin juyin mulki ke shugabanta.
Hukumomin Faransa sun sanar da mutanen cewa duk mai neman barin kasar, da ya dauki abin da bai fi karamar jaka daya ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa a birnin Paris ta bayyana cewa tashe-tashen hankula na baya-bayan nan da suka shafi ofishin jakadancin Faransa a Nijar ne dalilan da ya sa suke kwashe mutanen.
Matakin na zuwa ne a yayin wani rikicin da ya barke sakamakon juyin mulkin da aka yi wa zababben shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Baz...
- Title
- Abubuwa Da Dama Da Suka Faru Tun Bayan Da Sojoji Suka Yi Juyin Mulki A Nijar
- Runtime
- 5:33
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Tun bayan da sojoji masu gadin fadar shugaban kasa suka tsare shugaba Mohamed Bazoum a ranar Laraba 26 ga watan Yuli, sannan daga baya suka sanar da yin juyin mulki, abubuwa da dama sun faru.
- Title
- Tsohon Shugaban Amurka Trump ya ce ba shi da laifi a gaban kotun tarayya kan zargin zabe | VOA Hausa
- Runtime
- 0:30
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ki amsa laifinsa a wata kotun tarayya da ke birnin Washington domin fuskantar tuhuma kan yunkurinsa na yin watsi da rashin lashe zaben 2020.
Wani babban alkali ya tuhumi Trump da tuhume-tuhume guda hudu a cikin wannan makon, da suka hada da hada baki don damfarar Amurka, da hana aiki a hukumance da kuma hada baki don hana masu kada kuri’a hakkinsu na gudanar da sahihin zabe.
Trump ya musanta aikata ba daidai ba. Tun bayan da ya bar ofis, ya sha bayyana cewa zaben 2020 na magudin zabe ne, inda ya ce an gudanar da bincike a kansa duk na siyasa ne. Ya ci gaba da kasancewa babban ‘dan takarar neman takarar Republican a zaben shugaban kasa na 2024.
#Trump #DonaldTrump #usa #Republicans #January6 #Amurka #shorts #short #videoshort #videoshorts
Ku Bibiyi Shafin VOA Hausa YouTube: https://bit.ly/3Gcp7en
- - - - - -
Karin bayani akan VOA Hausa: https://www.voaha...
- Title
- Duba Tarihin Juyin Mulki A Jamhuriyar Nijar Tun Bayan Samun 'Yancin Kai
- Runtime
- 1:32
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Duba tarihin juyin mulki a kasar Nijar, wannan dai shi ne karo na biyar da sojoji ke yin juyin mulki tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960
- Title
- Sojojin Nijar Sun Sanar Da Abdourahmane Tchiani A Matsayin Jagoran Gwamnatin Kasar
- Runtime
- 1:07
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar sun sanar da kwamandan sojojin dake gadin fadar shugaban kasar ta Nijar Abdourahmane Tchiani a matsayin jagoran gwamnatin kasar.
- Title
- LAFIYARMU: Kalubalen Kaurar Da Likitoci Da Ma’aikatan Lafiya Ke Yi Daga Afirka Zuwa Kasashen Turai
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Karancin kwararrun ma'aikatan kiwon lafiya na shafar hanyoyin samun kulawar mutane, da ingancin kulawar da suke samu, da kuma yawan mutanen dake mutuwa sakamakon cututtuka a nahiyar.
- Title
- #TASKARVOA: Abubuwa Da Dama Da Suka Faru Tun Bayan Da Sojoji Suka Yi Juyin Mulki A Nijar
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Akan dambarwa dake faruwa a Nijar, mun samu tattaunawa da jakadan Nijar din anan Amurka, Mamadou Kiari Liman-Tinguiri, mun kuma duba taron gaggawa da Kungiyar ECOWAS ta yi a Abuja, Najeriya, da wasu rahotanni.
- Title
- Zanga-zangar Lumana Ta Kungiyar NLC a Abuja
- Runtime
- 4:17
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- NLC ta yi zanga-zangar lumana na nuna rashin aminta da halin da matakin cire tallafin mai ya jefa al’ummar Najeriya.
- Title
- Matakan Da Wasu 'Yan Najeriya A Jihar Kano Ke Dauka Na Rage Zafin Rayuwa
- Runtime
- 3:18
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Mun tattauna da Aminu Mahi, wani ma’aikacin gwamnati a jihar Kanon Najeriyan don jin irin matakin da shi ma yake dauka a wannan lokaci da farashin mai ke gagarar wasu mutanen, da kuma tashin farashin kayan masarufi.
- Title
- Hauhawar Farashin Kudin Mai Ya Sa 'Yan Najeriya Canji Zuwa Amfani Da Janaretan Gas
- Runtime
- 3:43
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Matsalar rashin ishasshiyar wutar lantarki da Najeriya ke fama da ita, ta sa mutane da dama dogaro da janareta. Sai dai cire tallafin mai ya sa farashin man fetur ya haura, lamarin da ya sa 'yan Najeriya suke canzawa zuwa janareta mai amfani da iskar gas.
- Title
- Kungiyar Kwallon Kafa Ta Mata Ba A Biyansu Daidai Da Takwarorinsu Maza
- Runtime
- 3:31
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Mata 'yan wasan kwallon kafa a Afirka kamar takwarorinsu na Amurka ba a cika biyansu daidai da takwarorinsu maza ba. Kungiyar kwallon kafa ta mata t Super Falcons ita ce ta fi kowacce kngiyar kwallon mata a nahiyar Afirka samun nasara inda ta lashe kofuna tara a cikin goma sha daya na nahiyar
- Title
- Yan Nijar Sun Shawarci Shugabannisu Da Su Rage Dogara Akan Kasashen Ketare
- Runtime
- 4:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Mahalarta wani taron muhawara da Muryar Amurka ta shirya a Yamai babban birnin Nijar, sun shawarci shugabannin kasar da su dauki kwararan matakai domin rage dogaro akan kasashen ketare ta fannin abinci da makamashi.
- Title
- #TASKARVOA: Cire tallafin mai a Najeriya ya kara tashin farashin kaya, mutane sun rage kashe kudi
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Halin matsin tattalin arziki da ake ciki a Najeriya sakamakon cire tallafin man fetur ya sa hukumomin kasar yin kokarin bunkasa amfani da wasu hanyoyin makamashi da ba na man fetur ba, abin da ya hada da canza injuna zuwa masu aiki da iskar gas da kuma fadada tashoshin cajin motoci masu amfani da lantarki.
- Title
- LAFIYARMU: Shin Me Ke Sa Ake Samun Karuwar Ciwon Bugun Jini A Tsakanin Matasa?
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Kwararru sun ce ana samun karuwar mutane masu kananan shekaru tattare da cutar bugun jini a fadin duniya sannan wasu dalilai da suke haifar da wannan yanayi sun hada da kiba mara kima, hawan jini da kuma cutar sukari wato diabetes.
- Title
- Yadda Wasu ‘Yan Nijar Ke Goyon Bayan Juyin Mulki a Kasar
- Runtime
- 2:18
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Yadda Wasu ‘Yan Nijar Ke Goyon Bayan Juyin Mulki a Kasar.
- Title
- Kungiyar Taliban Ta Bada Umarnin Rufe Shagunan Yin Kwalliyar Mata A Kasar
- Runtime
- 3:39
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Kungiyar Taliban ta ba da umarnin rufe shagunan yin kwalliyar mata a cikin wata guda. Masu shagunan da masu fafutukar kare hakkin mata sun bayyana matakin a matsayin mummunan koma baya ga mata a kasar.
- Title
- Tambayoyin 'Yan Najeriya Game Da Shirin Gwamnati Na Baiwa 'Yan Kasa Tallafin Kudi
- Runtime
- 5:33
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Wasu daga cikin tambayoyin da mutane a Najeriya ke yi a game da shirin gwamnati na baiwa wasu ‘yan kasa kudi a kowanne wata, sannan wadanne ka’idoji za a duba wajen zabo mutane miliyan 12 da za su amfana da tallafin?
- Title
- LAFIYARMU: Matsalar Rashin Samun Isasshen Barci Da Laluwar Da Hausawa Ke Kira Dannau A Cikin Barci
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Bisa binciken cibiyar kiwon lafiya ta Amurka, samun isashen bacci yana inganta yadda kwakwalwa take aiki, yanayin farin ciki da kuma lafiyar ka. Rashin sammun wadatacen bacci na kara barazanar kamuwa da cututtuka da matsalolin lafiyar jiki.
- Title
- #TASKARVOA: Tambayoyin da mutanen Najeriya ke yi a game da shirin gwamnati na ba wasu ‘yan kasa kudi
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kokawa da tsadar kayan masarufi, a makon jiya 'yan majalisar dokokin kasar suka amince da bukatar shugaba Bola Tinubu ta ciyo bashin dala miliyan 800 daga bankin duniya don taimakawa wajen rage radadin cire tallafin man fetur, da wasu rahotanni
- Title
- Wasu Kasashen Na Shirye-shirye Kwashe, Adana Kayan Al'adun Sudan
- Runtime
- 4:36
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Hukumomi da kungiyoyi a wajen Sudan su na hanzarin tsara shirye-shiryen kwashe kayayyakin tarihi da ake ta sace wa zuwa wuraren adanawa.
- Title
- Nan Da farkon Shekara Za A Fara Biyan Kudin Rage Cunkoson Ababen Hawa A Birnin New York
- Runtime
- 4:09
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Nan da farkon shekara mai zuwa za a fara aiki da sabon tsarin biyan kudi na rage cinkoson ababen hawa a tsakiyar Manhattan na birnin New York a nan Amurka
- Title
- Yadda Matsalolin Rashin Wutar Lantarki A Najeriya Ya Shafi Kiwon Lafiyar Jama'a
- Runtime
- 3:59
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Illolin matsalar wutar lantarki a Najeriya ba su tsaya kawai ga hana ci gaban tattalin arziki ba, har ma da bangaren kiwon lafiya.
- Title
- Tasirin Sabuwar Tashar Lantarki Daga Hasken Rana A Nijar
- Runtime
- 4:34
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Mun tattauna da Moustapha Kadi Oumani wani mai fafutukar ganin an wadata jama’a da lantarki a Nijar, a game da tasirin sabuwar tashar lantarki daga hasken rana.
- Title
- Manoma A Ghana Sun Rungumi Sabbin Hanyoyin Rage Lalacewar Kayan Gonakinsu
- Runtime
- 3:57
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Manoma a Ghana sun rungumi sabbin hanyoyin rage lalacewar kayan gonansu bayan girbi da kuma bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga.
- Title
- Shugaba Bazoum Ya Kaddamar Da Tashar Wutar Lantarki Mai Karfin Megawat 30
- Runtime
- 4:42
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya kaddamar da tashar samar da wutar lantarki mafi girma a kasar mai megawat 30, wanda zai kai ga gidaje 70,000, ko kuma mutane 500,000 a Yamai babban birnin kasar.

