VOA Hausa
LAFIYARMU: Abin Da Ke Haifar Da Mummunar Ciwon Koda
- Title
- LAFIYARMU: Abin Da Ke Haifar Da Mummunar Ciwon Koda
- Runtime
- 4:53
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Hukumar lafiya ta duniya ta kiyasta kiyasta cewa mutane miliyan 850 ne suke fama da cutar koda a fadin duniya, sannan cutar ta na sanadiyyar mutuwar sama da mutum miliyan 2 da dubu dari shida a kowace shekara.
- Title
- TASKAR VOA: Fiye da mutane miliyan 25 a Najeriya za su iya fuskantar matsalar rashin abinci - MDD
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- TASKARVOA: A Jamhuriyar Nijar ma, manoma da dama na fama da kalubalen sauyin yanayi, inda wasunsu suke barin aikin gona suke komawa ga wasu harkoki kamar hakkar ma’adinai, da wasu rahoranni
- Title
- LAFIYARMU: Kasar Malawi Na Samun Karuwar Wadanda Suke Kamuwa Da Cutar Kwalera
- Runtime
- 3:02
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Wannan na zuwa ne wattani 2 bayan da gwamnatin kasar ta janye matakin gaggawar lafiyar al’umma wanda aka ayyana tun shekarar 2022.
- Title
- TASKAR VOA: Hukumomin Najeriya Za Su Kafa Sabuwar Dokar Sa Ido AKan Shafukan Sada Zumunta A Kasar
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- TASKAR VOA: Nijar za ta fara fitar da gangan danyen mai dubu 90 domin siyarwa a kasuwannin duniya; Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta dauki tsauraran matakan tsaro na tabbatar da zabukan da aka gudanar ranar Asabar sun kammalu lami lafiya, da wasu rahotanni
- Title
- Masu goyon bayan Falasdinu suka yi kokarin kutsawa wani sansanin sojin Amurka a Ankara
- Runtime
- 1:00
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- 'Yan sandan Turkiyya sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwa yayin da daruruwan mutane masu goyon bayan Falasdinu suka yi kokarin kutsawa wani sansanin sojin Amurka ranar Lahadi, sa'o'i kadan kafin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Ankara domin tattaunawa kan Gaza.
- Title
- LAFIYARMU: Hira Da Dr Ibrahim, Kwararen Likitan A Najeriya
- Runtime
- 3:48
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Wani kwararen likita a Najeriya, Dr Ibrahim ya yi karin haske a game da fida da mutum-mutumi.
- Title
- LAFIYARMU: Yadda Ake Amfani Da Mutun Mutumi A Aikin Tiyata, Wato Robotic Surgery
- Runtime
- 4:29
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- A Afirka ta Kudu, an rungumi amfani da mutun-mutumi a aikin tiyata a zaman wani abin dogaro da shi nan gaba a fannin kiwon lafiya.
- Title
- TASKAR VOA: 'Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Kokawa Akan Mummunar Faduwar Darajar Naira Da Tsadar Rayuwa
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- TASKAR VOA: Yayin da darajar Naira a Najeriya ta yi mummunar faduwa, ‘yan kasuwa na kokawa da tsadar dala, mutanen gari kuma na kokawa da tsadar kayan masarufi, da wasu rahotanni
- Title
- LAFIYARMU: Yadda Ake Amfani Da Mutum Mutumi A Aikin Tiyata Wato Robotic Surgery
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- A Afirka ta Kudu, an rungumi amfani da mutun-mutumi a aikin tiyata a zamanin wani abin dogaro a gaba a Fanin kiwon lafiya.
- Title
- VOA Hausa: Yadda Masu Fasfo na Wasu Kasashe Suka Ketara Daga Gaza Zuwa Masar
- Runtime
- 0:16
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- VOA Hausa: Dimbin masu rike da fasfo na kasashen waje sun shiga mashigar kan iyakar Rafah daga Gaza zuwa Masar.
- Title
- VOA Hausa: Isra’ila ta kai hari kan Lebanon bayan da aka harba makamın roka
- Runtime
- 0:30
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- VOA Hausa: Isra’ila ta kai hari kan Lebanon bayan da aka harba makamın roka
- Title
- LAFIYARMU: Kafewar Jinin Al’ada Na Mata ,Daukewar Sha’awa Da Kuma Daukewar Kwayoyin Haihuwa A Maza
- Runtime
- 5:57
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shirin ya mafia hankalo kan kafewar jinin al’ada na mata wato menopause da kuma daukewar sha’awa da kwayoyin haihuwa a maza wato Andropause.
- Title
- LAFIYARMU: Kafewar Jinin Al’ada Na Mata, Daukewar Sha’awa Da Kuma Daukewar Kwayoyin Haihuwa A Maza
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Ana danganta kafewar jinin haila wato menopause da yawan jin zafi, gumi, yawan fushi da kuma sauyin lokacin saukar jinin al’ada. Andropause anayi ne da ake masa la’abi da “menopause din maza” wanda kehaifar da gagarumin sauyi a yanayin daidaituwar sinadarin hormones da kuma lafiyar jikin maza.
- Title
- Kimanin yara miliyan ashirin ne aka kiyasta ba sa zuwa makaranta a Najeriya - Kwararru
- Runtime
- 29:45
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- TASKAR VOA: Yayin da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta sanya wa Nijar ke kara tsananta matsalar abinci a kasar, hukumomi tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta SWISSAID su na kokarin karfafa samar da wadataccen abinci a kasar ta hanyar bunkasa noman rani da wasu sauran rahotanni
- Title
- Ta ya ya makari na Iron Dome yake aiki? #short #shorts
- Runtime
- 1:10
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Isra'ila na dogaro ne da makarin harin rokoki da ake kira ‘Iron Dome’ wajen kare 'yan kasarta daga hare-hare.
Makari na Iron Dome yana daya daga cikin muhimman makamai da Isra'ila ke amfani da su wajen kakkabo makaman rokoki.
Ta ya ya makari na Iron Dome yake aiki?
Makarin na Iron Dome na da karfin da zai iya kare harin makami mai linzami daga nisan kilomita hudu zuwa 70.
Da zarar na’ura ta Iron Dome ta gano wani abu na tafe, nan da nan za ta aika da sakon hanyar da abin ke tahowa zuwa wata cibiya.
Cibiyar za ta auna ta ga ko abin da ke tafe na tattare da wata barazana.
Ana amfani da yanayin hanyar da abin ya biyo da kuma irin gudun da yake yi wajen daukan mataki na gaba.
Akan yi watsi da rokokin da suka nufi yankunan da babu kowa.
Idan kuma aka ga rokokin sun nufi inda jama’a ke zaune, makarin na Iron Dome zai yi maza ya harba wasu makamai...
- Title
- Hukuncin Kotun Koli Kan Zaben Najeriya Na 2023
- Runtime
- 3:12
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Kotun mai mambobi bakwai karkashin jagorancin mai shari’a John Inyan Okoro a karshen zamanta ta yi watsi da karar da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da wanda Peter Obi na jam'iyyar Leba suga shigar na kalubalantar nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga Fabrairu, 2023.
- Title
- An Fara Samun Dogon Layin Sayan Mai A Birnin Abuja
- Runtime
- 2:07
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Mazauna babban birnin Abuja musamman direbobi sun fara kokawa kan yadda layukan mai suka fara tsawaita a birnin.
Kamfanin main a NNPCL ya fitar da sanarwa cewa, rashin wadatar man ya faru ne sakamakon tsaiko da aka samu.
- Title
- LAFIYARMU: Batun Wayar Da Kan Al’umma Game Da Cutar Dajin Mama
- Runtime
- 5:45
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shirin lafiyarmu na wannan makon, ya mai da hankali akan cututtukan Kansar da suka fi addabar mata a fadin duniya.
- Title
- LAFIYARMU: Yadda Sabon Maganin Rigakafin Zazzabin Maleriya Zai Iya Ceto Miliyoyin Rayuka
- Runtime
- 3:27
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Hukumar Lafiya Ta Duniya ta sahalewa sabon maganin rigakafin zazzabin cizon sauro. Ana fatan za a gaggauta fitar da sabon maganin a kasashen Afirka a cikin watanni masu zuwa.
- Title
- LAFIYARMU: Batun Wayar Da Kan Al’umma Game Da Cutar Dajin Mama
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane dubu dari shida da tamanin da biyar ne suka rasa rayukan su a dalilin cutar kansar mama a shekarar 2020 a fadin duniya. Hukumar ta ce an gano wasu mata miliyan 2.3 dauke da cutar ta cancer cikin wannan shekarar.
- Title
- TASKAR VOA: ‘Yan sanda a Najeriya su na ci gaba da bincike akan wani likita dake sace kodojin mutane
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- TASKAR VOA: Wasu daga cikin kurakuren da marasa lafiya ke samu a wajen duba lafiyarsu a Najeriya, ana danganta su ne da rashin kwarewar jami’an lafiya ko kuma shagunan magani na cikin unguwa, wasu rahotanni
- Title
- Gwamnatin Filato Za Ta Ci Gajiyar Ilimi Da Arzikin ‘Yan Jihar Mazauna Amurka
- Runtime
- 5:08
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Gwamnatin jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ta soma wani yunkuri domin ganin jama’ar jihar sun amfana daga ilmi, arziki, wayewa da fasahar ‘yan asalin jihar da ke zaune a Amurka da ma sauran kasashen duniya. Gwamna Caleb Mutfwang na jihar ne ya sanar da hakan a yayin babban taron kungiyar ‘yan jihar ta Filato mazauna Amurka na 2023.
- Title
- Bidiyon Harin Jirgi Mara Matuki: Yadda Harin Isra’ila Ya Lalata Unguwanni A Yankin Gaza #short
- Runtime
- 0:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai a Gaza a ranar Talata bayan ta lashi takobin daukar fansar da "da alumomin da ke tafe za su samu labari" kan kungiyar ta Hamas a harin ba-zata da ta kai a karshen mako.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan daruruwan wurare a unguwar Rimal da ke birnin Gaza, gundumar da ke da cunkoson jama'a, kuma gundumar da ke da ma'aikatun gwamnatin Hamas, da jami'o'i da kungiyoyin yada labarai da kuma ofisoshin kungiyoyin agaji.
Bayan sa’o’i ana ruwan bama-bamai babu kakkauta wa, wasu mazauna garin sun bar gidajensu da hantsi, inda suka tarar da wasu gine-gine sun ruguje sanadiyyar harin daga bama-baman, yayin da wasu kuma suka koma tamkar tuddun siminti. - AP
#israel #palestine #gaza #reels #igreels #videography #voa #hamas
- Title
- LAFIYARMU: Shin Wasu Kalubale Ne Masu Lalurar Zabiya Ke Fuskanta?
- Runtime
- 3:50
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Usman Audu, wani mai lalurar zabiya a birnin Maiduguri na Najeriya, ya yiwa Muryar Amurka karin bayani a game da kalubalen da suke fuskanta.
- Title
- LAFIYARMU: Matsalolin Da Mutane Zabaya Ke Fuskanta A Afirka
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Lalurar zabiya ta na shafar mutane a duniya ba tare da la'akari da kabila, ko jinsi ba. Lalurar ta na samuwa ne ta hanyar gado inda jikin mutun yake da karancin sinadarin melanin, wanda ya shafi launin fatar mutun.
- Title
- #TASKARVOA: Mayakan Kungiyar Hamas Sun Kai Wani Harin Bazata Akan Isra'ila Da Ya Ta Da Zaune Tsaye
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Kamar sauran kasashen duniya, mutane a Jamhuriyar Nijar na ci gaba da mayar da martani ga abubuwan dake faruwa tsakanin Isra’ilar da Falasdinawa; haka kuma a wasu manyan biranen duniya kamar babban birnin New York a Amurka mutane suna mayar da martani ne ga rikicin Isra'ila ta hanyar yin zanga-zangar nuna goyon baya ga bangarorin biyu, da wasu rahotanni
- Title
- LAFIYARMU: Lafiyar Tsofafi Da Yadda Za A Bunkasa Kula Da Lafiyar Su
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Kwararu sun ce asa’ilin da shekarun mutane suke ja, ya yiwu su fuskanci matsalolin lafiyar da suka zama ruwan dare tsakanin dattawa kamar yanar ido, rashin ji, cutar sukari, ciwon baya da na wuya.
- Title
- #TASKARVOA: Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun janye yajin aiki bayan cimma yarjejeniya da gwamnati
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Acewar bankin duniya, a 2022, mutane miliyan 64 ba su da asusun ajiyar kudi na banki, wadanda kuma suke da asusun ajiya a banki sukan fada cikin tarkon ‘yan damfara ta intanet; A karon farko a tarihin Amurka, an tsige kakakin majalisar wakilan kasar, da wasu rahotanni
- Title
- LAFIYARMU: Hira Da Wani Dattijo Mazaunin Abuja Mai Suna Tanko Yakasai
- Runtime
- 1:56
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Wani dattijo mazaunin Abuja mai suna Tanko Yakasai, ya tassama shekaru 100 a duniya. Yayi mana bayani game da yadda yake kula da lafiyar shi.
- Title
- LAFIYARMU: Lafiyar Tsofafi Da Yadda Za A Bunkasa Kula Da Lafiyar Su.
- Runtime
- 3:15
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Kwararu sun ce asa’ilin da shekarun mutane suke ja, ya yiwu su fuskanci matsalolin lafiyar da suka zama ruwan dare tsakanin dattawa kamar yanar ido, rashin ji, cutar sukari, ciwon baya da na wuya.
- Title
- LAFIYARMU: Ana Zargin Tsofafi A Wasu Al’ummomi A Kasashen Afirka Da Maita
- Runtime
- 3:40
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Majalisar dokokin Ghana ta kada kuri’ar da za ta bada dama a hukunta duk wanda ya zargi tsofafi da maita. Idan akayi nasarar tabbatar da sabuwar dokar, za ta bada dama a rufe sansanonin da sama da mutane 500 da ake zargi da maita.
- Title
- Spain, Portugal, Morocco, Argentina, Paraguay da Uruguay za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya
- Runtime
- 1:14
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Za a buga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2030 a Turai da Afirka, sannan kuma abin mamaki, an yi karin Kudancin Amurka a yarjejeniyar ba da damar daukan gasar kwallon kafa ta maza da a fara yayin bikin cika shekaru 100 a Uruguay.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta cimma yarjejeniya a ranar Laraba tsakanin shugabannin kungiyoyin kwallon kafar don karbar dan takara daya kacal domin karbar bakuncin gasar ta 2030 a kasashe shida, in ji hukumar wasanni.
Tayin Spai da Portugal na daukar nauyin gasar ya karu da karin Morocco a wannan shekara kuma yanzu haka ya hada da kishiyoyinsu Argentina da Paraguay da Uruguay da suka dade suna neman tikitin. FIFA ta ce dukkan kungiyoyin kasashe shida za su samu shiga gasar da ta kunshi kungiyoyi 48.
Wani muhimmin abin burgewa na hadin nahiyoyi uku da ba a taba ganin irinsa ba shi ne, budewar gasar a babban birnin kasar Uruguay na Montevideo, inda filin wasan Centenario ya karbi bakuncin wasan karshe na gasa...
- Title
- 'Yan Majalisa Sun Kada Kuri'ar Tsige Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Daga Mukaminsa #short
- Runtime
- 0:34
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Dan majalisar wakilai Kevin McCarthy, dake wakiltar jihar California, Ya bar zaman majalisar bayan da aka tsige shi a matsayin kakakin Majalisa a birnin Washington.
A karon farko a tarihin Amurka, ‘yan Majalisar Dokokin Amurka sun kada kuri’a a jiya Talata don tsige kakakin Majalisar Wakilan Amurka daga mukaminsa.
‘Yan majalisa 216 ne suka amince a tsige Kevin McCarthy dan jam'iyyar Republican daga mukamin kakakin majalisar yayin da wasu 210 suka yi akasin haka, sakamakon sukar ba sabam ba da ya fuskanta daga jam'iyyarsa.
Dan majalisar wakilai na jam'iyyar Republican Matt Gaetz ne ya gabatar da kudurin a yammacin ranar Litinin don tilasta kada kuri'a kan tsige McCarthy, yana mai bayyana takaici kan shugabancin McCarthy bayan da McCarthy ya kasa zartar da kudirin kasafin kudin Gwamnati da ya dada wa ‘yan Republican masu ra'ayin mazan jiya a makon da ya gabata.
- Title
- Bakin Haure “Daga Afirka da Sauran Sassan Duniya” sun Taru a Tsakanin Shingayen Kare Iyakokin Amurka
- Runtime
- 0:41
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Daruruwan bakin haure ne suka taru a tsakanin shinge biyu na kan iyakar Amurka da Mexico kusa da San Diego, California, suna jiran Hukumar Kwastam da Kariya ta Amurka ta tantance su. Jami’an agaji sun ce bakin hauren sun fito ne daga kasashen yammacin Afirka da Amurka ta tsakiya da kuma Asiya. - Reuters
#migrants #border #usborder #sandiego #ghana #africa #voa
- Title
- Wakilai Daga Kasashe 100 Su Na Halartar Bikin Raya Al’adu Na 2023 A Amurka
- Runtime
- 2:30
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Wakilai daga kasashen duniya kimanin dari su na halartar babban bikin raya al’adu na 2023 dake gudanar a birnin Washington DC na Amurka. Bikin na kwana uku ya kunshi raye-raye da kade kade da kuma baje kolin abincin al’adun mutane daban daban.
- Title
- #TASKARVOA: Matsalar Yawan Sace Dalibai Da 'Yan Bindiga Ke Yi A Najeriya
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Yayin da kamfanoni da sauran masu sana’o’i ke ci gaba da tafka asara sakamakon karancin wutar lantarki a Nijar, wasu kugiyoyin fararen hula a kasar sun yi barazanar maka Najeriya a gaban kotun ECOWAS kan zargin saba yarjejeniyar kasuwancin wutar lantarki tsakanin kasashen biyu, da wasu rahotanni
- Title
- LAFIYARMU: Amfani, Aminci Da Tasirin Magugunan Gargajiya, Wajen Kula Da Lafiya
- Runtime
- 2:11
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Maganin gargajiya ya kunshi abubuwa da dama na gargajiya da na zamani wanda ya samo tushe daga al’adun gargajiya da ake amfani da su tun iyaye da kakanni wajen kariya, ganowa da kuma magance jerin cututtuka na bayyane da kuma cututtukan tabin hankali, a cewar kungiyar hukumar ta Duniya WHO.
- Title
- Masu zanga-zangar sun hau tituna a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Na 78 #short #shorts
- Runtime
- 0:27
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Masu zanga-zangar sun hau tituna a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Na 78
Yayin da ake gudanar da Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, masu zanga-zanga da ke wakiltar manufofi da kasashe daban-daban sun yi tattaki a titunan New York.
Shugabannin kasashe daban-daban na duniya sun hallara a birnin na New York na kasar Amurka domin halartar Babban Taron wanda aka fara ranar Talata.
#unga #voaunga #unga78 #voahausa
- Title
- Antonio Guterres Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya: Duniyar Mu tana zama 'a jirkice' #short
- Runtime
- 0:26
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shugabannin duniya da ke fama da yaƙe-yaƙe, sauyin yanayi da kuma rashin daidaiton da ake ci gaba da yi sun taru wuri daya yau Talata don jin shugaban Majalisar ɗinkin duniya yana kiran su da su ɗauki mataki na bai ɗaya kan manyan ƙalubalen da ke fuskantar bil adama - da kuma fara gabatar da nasu kima a kan mafi manyan matakai na duniya.
"Duniyarmu tana komawa a jirkice. Tashin hankali na yanayin siyasa yana karuwa. Kalubalen duniya suna ta karuwa. Kuma da alama ba za mu iya haduwa don mayar da martani ba, ”Antonio Guterres ya fadawa mutanen da ke tafiyar da kasashen duniya.
#unga #voaunga #unga78 #AntonioGuterres
- Title
- Jawabin Shugaban Guinea Mamady Doumbouya a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya #short #shorts
- Runtime
- 0:57
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Jawabin Shugaban Guinea Mamady Doumbouya a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban rikon kwarya na Guinea, Mamady Doumbouya, a jawabin da ya yi a taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, ya ce tsarin mulkin dimokradiyya "ba ya aiki" a Afirka.
#unga #voaunga #unga78
- Title
- Yayin jawabinsa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
- Runtime
- 0:23
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan "gazawa wajen samar da shugabanci nagari wanda hakan ke kawo cikas ga ci gaban Afirka", sannan ya yi nuni da yadda ake "karya alkawura da rashin adalci" da wasu kasashen waje ke yi, wanda hakan "ya durkusar da nahiyar a fannin ci gaba.” -AFP
#unga #voaunga #UNGA78 #Tinubu #Nigeria #Africa
- Title
- LAFIYARMU: Hira Da Abdulshahid Sarki, Kwararren Likita A Asibitin Kasa Dake Abuja
- Runtime
- 5:19
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Abdulshahid Sarki, Kwararren likita a asibitin kasa dake Abuja, ya yi mana bayani a game da matakan da suka kamata mutane su dauka don tunkarar al’amari na daukin gaggawa.
- Title
- LAFIYARMU: Wani Irin Tasiri Ayyukan Gaugawa Na Lafiya Suke Da Shi A Cikin Al’ummar Ku?
- Runtime
- 3:17
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Ra’ayoyin wasu mutane daga Najeriya game da irin matakan gaggawa da suke dauka na taimakon kan su idan bukata ta taso.
- Title
- #TASKARVOA: Yadda Shugabannin Kasashen Duniya Suka Gabatar Da Jawabansu A Taron UNGA
- Runtime
- 29:46
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- #TASKARVOA: Yadda shugabannin kasashen duniya suka gabatar da jawabai da suka tabo batutuwa daban-daban a wurin babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ya gudana a birnin New York na Amurka; Karin haske akan hukuncin da kotun kararrakin zabe a Kano ke nunawa, da wasu rahotanni
- Title
- Yiwa Shugabanni Addu’a Shi Ne Zai Hana Su Lalacewa - Gawuna
- Runtime
- 9:48
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki a zaben watan Maris a jihar Kano wanda kotun sauraron kararrakin zabe a Kano ta baiwa nasara ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da muryar Amurka a birnin tarayya Abuja.
- Title
- LAFIYARMU: Bukatun Kula Da Lafiya Da Ke Tasowa Bayan Aukuwar Wani Bala’i Ko Mummuman Lamari
- Runtime
- 15:01
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Bala’o’I na iya faruwa kwatsam, a ko yaushe ba tare da wani shiri ba.
Mummunar guguwa, ambaliyar ruwa da girgizar kasa na daga cikin bala’o’in da suke aukuwa da suke jefa al’umma cikin tashin hankali.
- Title
- Antonio Guterres, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya: Duniyar Mu tana zama 'a jirkice' #short
- Runtime
- 0:26
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shugabannin duniya da ke fama da yaƙe-yaƙe, sauyin yanayi da kuma rashin daidaiton da ake ci gaba da yi sun taru wuri daya yau Talata don jin shugaban Majalisar ɗinkin duniya yana kiran su da su ɗauki mataki na bai ɗaya kan manyan ƙalubalen da ke fuskantar bil adama - da kuma fara gabatar da nasu kima a kan mafi manyan matakai na duniya.
"Duniyarmu tana komawa a jirkice. Tashin hankali na yanayin siyasa yana karuwa. Kalubalen duniya suna ta karuwa. Kuma da alama ba za mu iya haduwa don mayar da martani ba, ”Antonio Guterres ya fadawa mutanen da ke tafiyar da kasashen duniya.
#unga #voaunga #unga78 #AntonioGuterres
- Title
- Shugaba Joe Biden ya yi jawabi a gaban shugabannin kasashen duniya a babban taron MDD
- Runtime
- 0:21
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- “Amurka za ta ci gaba da kokarinta na rage barazanar makaman kisan kare dangi. Ko da me ke faruwa a duniya. A wannan shekarar, mun kawar da tarin makaman guba na ƙarshe, da Amurka ta ajiye, inda muka cika alƙawarinmu na kawar da makaman guba a duniya.“
#unga #voaunga #unga78 #biden #AU #AfricanUnion #ECOWAS #MDD #JoeBiden
- Title
- Biden Ya Yi Allah Wadai Da Juye-juyen Mulki A Afirka, Ya Na Mai Jaddada Tafarkin Dimokradiyya
- Runtime
- 0:34
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Shugaban Amurka Joe Biden a jiya Talata ya yi jawabi a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 da ake kira UNGA a takaice, inda ya tabo batutuwa da dama, ciki har da muhimmancin mutunta kimar dimokradiyya da kuma batun juyin mulkin soja a Afirka.
Yayin da yake gabatar da jawabinsa Biden ya ce Amurka "ta kira babban taron kolin dimokradiyya don karfafa gwamnatocin dimokradiyya, da kawar da cin hanci da rashawa, da kuma kauce wa tashin hankalin siyasa," ya kara da cewa, "kuma a halin yanzu, da ake hambarar da shugabannin da aka zaba ta hanyar dimokradiyya a yammaci da tsakiyar Afirka a-kai-a-kai, hakan na tunatar da mu cewa aikin da ke gabanmu na da matukar muhimmanci ya na kuma bukatar matakin gaggawa."
#unga #voaunga #unga78 #biden #AU #AfricanUnion #ECOWAS #MDD #JoeBiden
- Title
- LAFIYARMU: Kwararru Sun Ce Auren Wuri Yana Tasiri Ga Lafiya Da Rayuwar ‘Yaya Mata
- Runtime
- 4:00
- Date posted
- 3 years ago
- Description
- Alkaluman sun nuna cewa, yara mata da aka aurar da su a kananan shekaru sun fi kasancewa cikin hadarin fuskantar cin zarafin aure, da kasancewa cikin hadarin kamuwa da cututtukan zuciya, cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar mu’amalar aure (jima’i), matsalar tabin kwakwalwa da kuma haihuwa.

